Cristiano Ronaldo ba zai buga wasan da Manchester United za ta yi da Chelsea ba a ranar Asabar.
Dan wasan gaban Portugal ya bar Old TRafford kafin kallama wasan da ta yi da Tottenham ta samu nasara da ci 2-0 a ranar Laraba – saboda an barshi a benci ba a sa shi a wasan ba.
“Sauran ‘yan wasan kungiyar za su ci gaba da shirye-shirye na wasan gaba,” kamar yadda wata sanarwa da kungiyar ta fitar ta bayyana kamar yadda BBC ta ruwaito.
United ta ce dan wasan mai shekara 37 na da matukar muhimmanci a tawagar, sai dai wannan mataki ne da ya shafi kwamitin ladabtarwa.