BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Maganganun El-Rufai sun nuna ba dattijo ba ne-Bafarawa

Tsohon gwamnan Sokoto kuma jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Attahiru Bafarawa ya nuna rashin dadinsa game da kalaman da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasiru El Rufa’I ya yi, cewa babu sauran dattawa a arewacin kasar.

Attahiru Bafarawa ya ce waɗannan kalamai cin fuska ne kuma akwai rashin dacewa a ce El Rufai ya yi jam’i, saboda ai na kirki ba sa karewa.

Tsohon gwamnan ya mayar da martani ne a tattaunawarsa da BBC.

Gwamna Nasir Elrufa’I ya yi waɗannan kalamai ne a lokacin wata tattaunawa da BBC kan zargin da suke cewa akwai masu yi wa jam’iyyar zagon kasa, da ke fakewa da zance sauya takardun kuɗi domin ganin sun faɗi zaɓe.

Sannan El-Rufai ya ce, “Batun wani dattawa, ba wani dattawa, ni ma dattijo ne domin a wannan shekarar ta 2023 zan cika shekara 63, don haka su waye dattawan Arewa, mu gwamnonin Arewa mu ne dattawan Arewa kuma mune shugabannin Arewa.”

Attahiru Bafarwa ya ce ai shekaru, ba su ba ne dattako, domin akwai masu karancin shekaru amma kuma tunaninsa na manya ne da sanin ya kamata.

Bafarawa ya ce karami mai hankali, nagartacce ya fi mai shekara 100, in dai batun na shekaru ne.

“Sannan da ya ke magana cewa shekarun sa 63, kuma baya ganin da sauran dattijai a arewa, to mu muna ganin waɗannan maganganu akwai rashin dattijantaka a cikinsu.

“Kalaman Elrufa’I babu dattijantaka da girma a ciki, saboda abin da ya kamata ya yi shi ne, kalaman ci gaban arewa da ci gaban kasa da jama’a baki ɗaya.

“Sannan Elrufa’I na maganar ya tsaya zaɓe an zaɓe shi, idan wannan shi ne dattijo to ai tun kafin ya yi takara mu muka yi kuma aka zaɓe mu”, in ji Bafarawa.

Tsohon gwamnan ya ce, abin da Elrufa’I bai sani ba, shi ne arewa tafi karfin wani mutum guda, kuma duk mutumin da ya wulakanta ta ba zai gama lafiya ba.

“Saboda haka mu da ya ke ganin ba dattijai ba ne zai gane cewa akwai dattawa a arewa.”

Attahiru Bafarawa ya ce inda Elrufa’I ya bambanta abin da ya ke nufi da dattijai, ya ce ‘yan siyasa masu katsalanda, da babu mamaki ba zai tsaya mayar masa da martani ko mu sa zancensa ba.

Amma kuma duk lalacin abu akwai mai gyara shi, babu yadda za a yi, ya yi jam’i baki daya, sannan su zauna su na kallonsa, ba za su yarda ba.

“Idan ma akwai kalilan sai ya yi musu nasiha, amma ba wai jam’i ba baki ɗaya ba.

“Sannan ya fito yana dagewa da nanata cewa ko ana so ko ba a so su sun gama cin zaɓe, sai Tinubu ya ci zaɓe, to waya gaya masa cewa duk arewa APC ake yi.

“Wannan ra’ayinsa ne, don haka ba shi da ikon dagewa da sunan Arewa. Saboda ko wa na da ɗan takararsa.

“Yadda yake yi wa Tinubu kamfen, muma muna yiwa ɗan takararmu.”

Bafarawa dai ya jadada cewa, mutum ba shi da ikon dagewa cewa dole sai ya cusawa mutane ɗan takararsa, ko wani abu da ya zama kamar na dole.

“Za mu ba su mamaki, domin sai mun koya musu cewa kasar nan ba ta kowa ba ce, hakazalika arewa.”

Leave a Reply