Labarai

LABARAI’Yan Sanda Sun Dakile Zaben Fidda Gwanin PDP Kwankwasiyya A Kano

‘Yan sanda dauke da muggan makamai sun hana wani bangare na ‘yan jam;iyyar PDP karkashin wani shashi na Kwankwasiyya gudanar da zaben fid da gwamni a dai dai lokacin da ake gudanar da wani taron kuma na jam’’iyyar ta PDP a ranar Litinin a garin Kano. Daruruwan ‘yan akidar Kwankwasiyya suka halarta sakatariyar kungiyar dake ‘Lugard House’ tun da misalign karfe 6 na safe amma ‘yan sanda dauke da muggan makamai suka hana su shiga don gudana da taron. Sakatare na kasa na kungiyar Kwankwasiya ta ‘Kwankwasiyya Awareness Network’ Kwamrade  Auwal Muhammad, y ace, sun isa Lugard House ne tantance wakilai a shirye shiryen gudanar da zaben fid da gwani. “An sanar da dukkan wakilai ‘yan Kwankwasiyya da masu takarar su kasance a Lugard house a yau don a tantance su kafin a ci gaba da zaben fidda gwani. A wannan gidan ne muke haduwa don tattauna harkokinmu na siyasa, saboda haka ne muka gayyaci ‘yan kwankwasiyya da kuma ‘yan PDP daga kananan hukumomi 44 na jihar sai kawai muka zo muka tarada da ‘yan sanda sun garkame daki taron,” inji shi. A yayin da wakilinmu ya ziyaci Lugard House da dakin taro na Marhaba, ya lura da motocin ‘yan sanda na Hilud guda 7 a bangaren Marhabah yayin da guda 5 kuma sun garkame hanyar shiga da fita Lugard House. Da yake mayar da martini a kan lamarin, daya daga cikin shugabanin kungiyar, Alhaji Umar Haruna Doguwa, y ace, sun shirya gudanar da zaben fid da gwani a Marhaba, amma ‘yan sanda dauke da muggan makamai suka mamaye wurin siuka kuma hana su shiga don yin abin daya kawo su. Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa ya ce, sai dai in hedikwatar jam’iyyar ta yi wani abu daban amma lallai ba a yi wani zaben fid da gwani ba a jihar gaba daya. Ya kuma ce, sun bi dukkan ka’idojin da ya kamata a bi na gudanar da zaben fid da gwanin a jihar, ya ce, “kafin a gudanar da zaben sai an kafa kwamitin da zasu gana da ‘yan takara da kuma masu ruwa da tsaki amma a an nan kano duk baa bi wadannan tsarin ba gaba daya. “Kwamitin kuma zai zo da wasika guda 4 daya zuwa ga shugaban jam’iyya daya kuma zuwa ga jami’an rundunar ‘yan sanda daya kuma ga hukumar DSS yayin da za a ba daya ga hukumar zabe ta INEC ana sanar da su cewa,  za a gudanar da zabe, amma a namu karon ba a yi wani abu kamar hakar ba. “Su wanene ‘yan kwamitin, a ina suna yi taro da ‘yan takara, dole mu zauna mu warware lamarin maimako mu kara dagula wa kamu lamarin gaba daya. Babu abin da ba za a iya warware wa ta hanyar tattaunawa ba. Da yake tabbatar da faruwar lamarin, jami’in watsa labarai na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Magaji Musa Majia, ya ce ‘yansanda na bin umurnin kotu ne da ta haramta wa jam’iyyar PDP gudanar da zaben fida gwani da sauran harkokin zabe a cikin jihar gada day

Leave a Reply