Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso na daf da sake barin jam’iyar adawa ta PDP zuwa New Nigeria Peoples Party, NNPP.
Sakataren jam’iyar na ƙasa mai barin gado, Agbo Gilbert Major ne ya fasa ƙwai a kan shirin na Kwankwaso a yayin taron masu ruwa da tsaki na ƙasa da jam’iyar ke shirin yi a Abuja.
Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Major ya ce tuni Kwankwaso ya gana da shugabannin jam’iyar domin tsara sauya shekar ta sa zuwa NNPP.
Ya ƙara da cewa yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023 a kasar nan, akwai bukatar a yi wa jam’iyar NNPP garambawul, inda ya ƙara da cewa ƴan siyasa da dama na kan hanyarsu ta shigowa jam’iyar.