BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kwanan nan zan bayyana asalin rikicin PDP-Wike

Gwamna Nyesom Wike na Jihar Rivers Ribas ya ce nan ba da jimawa ba zai “fasa ƙwai” kan abubuwan da ke faruwa a tsakanin sa da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyar PDP, da ma rikicin jamiyyar gana ɗaya.

Wike ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da Kelvin Ebiri, mataimakinsa na musamman kan harkokin yada labarai ya sanya wa hannu a biya Asabar a Fatakwal.

Wike ya ce ya dace ya shaida wa ƴan ƙasa kan duk wani abu da ya faru a jam’iyyar, tun bayan samun takara da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi a jam’iyyar.

A cewarsa, “Akan Atiku, zan yi magana nan ba da jimawa ba, kuma ‘yan Nijeriya za su san gaskiyar duk abin da ya faru a PDP a ‘yan kwanakin nan.” Kamar yadda muka kalato daga Daily Nigerian Hausa.

Leave a Reply