BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kotun Ƙolin ta dakatar da CBN daga aiwatar da wa’adin amfani da tsofaffin kuɗi

Kotun Ƙolin Najeriya ta dakatar da gamnatin tarayya daga aiwatar da wa’adin amfani da tsoffin takardun kuɗin kasar.

A bayan dai CBN ya saka ranar 10 ga watan Fabrairu a matsayin ranar da za a daina amfani da tsoffin takardun 1,000 da 500 da kuma 200 da aka sake.

Jihohin arewacin ƙasar uku ne dai da suka haɗar da Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar da ƙarar a gaban Kotun Ƙolin ƙasar suna buƙatar kotun da ta hana Babban Bankin ƙasar aiwatar da wa’adin.

A hukuncin wucin-gadin da suka suka yanke, alƙalan kotun bakwai ƙarƙashin jagaorancin mai shari’a John Okoro, sun dakatar da gwamnatin tarayya da Babban bankin ƙasar da sauran bankunan kasuwanci na ƙasar daga aiwatar da wa’adin 10 ga watan Fabrairu na amfani da tsofaffin takardun kuɗin ƙasar.

Kotun ta kuma ce dole ne gwamnatin tarayya da CBN da kuma sauran bankunan ƙasar sun jingine batun aiwatar da wa’adin har zuwa lokacin da kotun za ta yanke hukunci game da lamarin ranar 15 ga watan Fabrairu, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Da wannan hukunci dai yanzu ‘yan ƙasar za su ci gaba da amfani da tsofaffin takardun kudin ƙasar.

Leave a Reply