Wata kotun majistare a jihar Kano ta aike da shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya Alhassan Ado Duguwa zuwa gidan yari bayan gurfanar da shi a gaban kotun.
Ana zargin ɗan majalisar da muggan laifuka ciki har da zargin aikata kisan kai da mallakar makami ba bisa ƙa’ida ba da hannu a kunna wuta a wani gini.
An gurfanar da shi tare da wani mutum wanda ake zargi sun haɗa baki wajen aikata kisan kai da tayar da zaune-tseye a ƙaramara hukumar Tudun wada da ke jihar ranar Asabar da ta gabata.
Alƙalin kotun ya ɗage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Maris domin duba buƙatar yiyuwar bayar da belin ɗan majalisar ko kuma akasin haka.