Kano Ayau Hausa, Siyasa

Kotu ta soke zaben fitar da gwanin APC a jihar Zamfara

Wata kotun daukaka kara da ke zamanta a jihar Sokoto ta soke hukuncin wata babbar kotu da ta bai wa jam’iyyar APC damar tsayar da dan takara a zaben da aka kammala a kasar.

A zaman kotun na ranar Litinin, alkalan da suka jagoranci shari’ar sun ce babbar kotun ta Zamfara da ta bai wa APC dama, ba ta yi nazari kan hujjojin da aka gabatar mata kamar yadda ya kamata ba.

Bangaren Sanata Kabiru Marafa da suka shigar da karar sun bayyana murna game da nasarar, sai dai lauyan da ya kare bangaren Gwamna Abdulaziz Yari ya ce za su yi nazari a kan hukuncin.

A zaman kotun daukaka karar a birnin Sokoto da ke arewacin Najeriya, alkalan kotun uku karkashin jagorancin Mai Shari’a Tom Yakubu, sun soke hukuncin babbar kotun ta Zamfara.

Kotun dai ta bai wa Alhaji Mukhtar Idris tsayawa takara a karkashin jam’iyyar APC, kuma ya lashe zaben da aka yi a ranar 9 ga wannan watan Maris kamar yadda BBC ta rawaito.

Alkalan sun ce babbar kotun ta Zamfara ba ta yi nazarin wasu hujjojin da aka gabatar mata ba sosai, yayin waccan shari’ar don haka kotun daukaka karar ta soke hukuncin.

Sai dai daya daga cikin lauyoyin da suka kare bangaren Gwamna Yari, Barista Junaidu Abubakar Gusau ya ce za su yi nazari a kan hukuncin kotun sannan su san mataki na gaba da za su dauka.

Rikicin cikin gida da jam’iyyar ta APC ke fama da shi a tsakanin banagarorin biyu ya shafi zaben fitar da gwani a jihar.

Lamarin da ya kai hukumar zabe ta INEC ta shaida wa uwar jam’iyyar cewa ba ta da dan takara saboda ba a yi zaben fitar da gwani ba a jihar, sai dai bangaren gwamnan jihar ya garzaya babbar kotu da aka soke hukuncinta a ranar Litinin.

Da alamu tsugune ba ta kare ba musamman idan bangaren Gwamna Yari ya yanke shawarar zuwa kotun koli.

Leave a Reply