GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Kotu ta hana DSS kama Gwamnan CBN bisa zargin ta’addanci

Alkalin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, mai shari’a John tsoho, ya yi watsi da bukatar Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) na samun izinin kama Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele kan zarginsa da daukar nauyin ‘yan ta’adda.

Tsoho ya yi watsi da bukatar DSS ne, inda ya ce ba su gabatar da hujja gamsasshiya da ke nuna Gwamnan na CBN na da hannun wajen daukar ayyukan ta’addanci a kasar nan ba.

“Saboda rashin gabatar da hujja, ba zan bayar da izini ga masu kara ba, idan kuma har akwai hujja, to su gabatar da ita don a ba su izinin ci gaba da aikinsu.

“Idan har sun dage dole ne su bayar da hujja mai karfi duba da ofishin da wanda ake kara yake rike da shi,” inji alkalin.

Kashe Ummita: Inda aka kwana kan shara’ar dan China

Ya kuma ce DSS ta gabatar da sunan Godwin Emefiele a matsayin wanda ta ke neman izinin kamawa, amma babu wata hujja a kansa.

Yunkurin DSS na damke Emefiele na zuwa ne bayan da Gwamnan na CBN, ya fito da sabon tsarin sauya fasalin takardun kudi na N200 da N500 da kuma N1,000, kamar yadda muka ruwaito daga Aminiya.

Har wa yau, gwamnan ya jadadda tsarin takaita yawaitar kudade a hannun mutane, wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen kawo karshen ta’addanci da kuma biyan ‘yan bindiga kudin fansa da mutane ke yi.

Wannan tsari dai ya sanya Majalisar Wakilai gayyatar Emefiele gabanta, don amsa tambayoyi game da manufar ta CBN.

Tun da farko majalisar ta yi watsi da tsarin, inda ta ce hakan na iya jefa mutanen karkara cikin tsaka mai wuya tare da kashe harkokin kasuwancinsu.

Leave a Reply