Wata kotun majistare da ke zamanta a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano da ke Kano a ranar Litinin ta yanke wa tsohuwar jarumar fina-finan nan ta Kannywood, Sadiya Haruna, hukuncin daurin wata shida ba tare da zabin tara ba.
An dai gurfanar da ita ne a gaban kotun bisa zargin bata sunan wani tsohon saurayinta, kuma mawaki a masana’antar, Isa A. Isa.
A bara ce Sadiya Haruna ta zargi Isah A. Isah da yi mata ciki da tursasa ta zubar da cikin.