BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kotu ta ba Ahmed Lawal takarar sanata

Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da Sanata Ahmad Lawan matsayin halastaccen ɗan takarar kujerar sanata ta Yobe ta arewa.

Da yake yanke hukuncin alƙalin kotun mai shari’a Centus Nweze ya ce Bashir Machina ya gaza gabatar wa babbar kotun tarayya da ke Damaturu hujjar – baka ta zargin aikata maguɗi a zaɓen fitar da gwanin – da ya sa ake gayyatar ɓangaren Ahmad Lawan zuwa kotun.

Jam’iyyar APC ce dai ta ƙalubalanci Bashir Machina a matsayin ɗan takararta na kujerar sanatan Yobe ta Arewa, tana mai cewa Ahmad Lawan ta sani a matsayin halastaccen ɗan takara.

A zaman sauraron ƙarar da ya gabata, lauyan jam’iyyar Sepiribo Peters ya ce zaɓen fitar da gwanin da ya bai wa machina nasara, ya saɓa wa dokar zaɓe ta 2022.

Peters ya ce ba jam’iyyar ce ta naɗa Danjuma Manga a matsayin jami’in da ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin ba.

Ya shaida wa kotun cewa jam’iyyar APC ta soke zaɓen fitar da gwanin sakamakon matsalolin da aka samu a lokacin gudanar da zaɓen, inda a cewarsa kwamitin gudanarwar jam’iyyar ya sake shirya wani zaɓen fitar da gwanin ranar 9 ga watan Yuni, inda kuma Ahmad Lawan ya yi nasara, kamar yadda BBC ta ruwaito.

To sai dai lauyan Bashir Machina Sarafa Yusuf ya ce Shugaban Majalisar Dattawan bai ƙalubalanci hukuncin da kotunan baya suka yi ba.

Ya ƙara da cewa mutumin da ya jagorancin zaɓen da ya bai wa machina nasara mamba ne a kwamitin gudanarwar jam’iyyar, wanda kuma aka naɗa domin ya jagoranci zaɓen fitar da gwanin.

Leave a Reply