BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kasafin Kudin Buhari na karshe ya zarce Triliyan 19

Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya ce a makon farko na watan Oktoba mai kamawa ake sa ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai gabatar da kasafin kudin 2023 da ya kai Naira tiriliyan 19.76
Ya ce matukar ba a sami canjin tsare-tsare ba, Shugaban zai gabatar da daftarin kasafin wanda shi ne zai kasance na karshe a wa’adin mulkinsa, a gaban zauren Majalisar Dokoki ta Kasa.
Gwamnatin Tarayya dai ta tsara kashe Naira tiriliyan 19.76 kamar yadda yake kunshe a daftarin kashe kudade na matsakaicin zango (MTEF) wanda aka gabatar wa majalisar a kwanakin baya kamar yadda muka kalato daga Aminiya.
Gbajabiamila ya bayyana haka ne ranar Laraba a Abuja, lokacin da ya kammala duba aikin yin kwaskwarima ga ginin harabar Majalisar Dokokin da ake yi.

Leave a Reply