BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kano Ta Fara Biyan Dalibai Mata Albashin N20,000

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da fara biyan albashin N20,000 a duk wata ga dalibai mata 45,000 da ke ƙananan makarantu da nufin ba wa iyayensu ƙwarin gwiwar tura ’ya’yansu mata makaranta.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sanar cewa gwamnatin jihar ta fara biyan daliban, kuma nan ba da jimawa ba za ta dawo da shirin ciyar da dalibai da kuma motocin ɗaukar daukar su kyauta.

“Domin bunkasa karatun ’ya’ya mata da ba wa iyayensu kwarin gwiwar tura su makaranta, mun fara shirin gwaji na biyan N20,000 ga dalibai mata sama da 45,000 domin taimaka wa iliminsu.

“Za mu dawo da shirin ciyar da dalibai da kuma motocin daukar dalibai kyauta zuwa makaranta da kuma dawo da su,” in ji shi a jawabinsa na ranar cikar Najeriya shekara 63 da samun ’yanci kamar yadda muka kalato daga Aminiya.

Ya ce gwamnatin Kano na gina sabbin makarantu a duk kananan hukumomi 44 da ke jihar na nufin ganin yaran da ke gararamba a titi sun koma aji.

Abba ya kuma jaddada shirin gwamnatin Kano na tura dalibai 1,001 da suka kammala digirin farko da daraja ta daya zuwa kasashen waje domin karo ilimi.

Leave a Reply