Kamfanin man fetur na Najeriya ya tabbatar da cewa ya ƙara kuɗin litar mai a ƙasar.
A wata sanarwa da ta kamfanin ya wallafa a shafinsa na twitter, kamfanin ya ce ya yi ƙarin farashin domin yin daidai da halin da ake ciki.
Kuma ya roƙi afuwa kan wahalhalun da hakan zai iya haifarwa.
Hakan dai na zuwa ne bayan shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya sanar, a lokacin rantsar da shi cewa gwamnati ta dakatar da tallafin.
Ya ce “Tallafin mai ya tafi.”
Tun bayan furucin sabon shugaban ƙasar ne aka fara ganin dogayen layuka a gidajen mai, yayin da kowane gidan mai ke sayar da man a farashi daban-daban.
Ita ma, Ƙungiyar Dillalan Man Fetur masu Zaman Kansu ta Najeriya (IPMAN), ta fitar da sabon farashin da gidajen mai za su rinƙa sayar da litar mai a faɗin ƙasar.
A cewar ƙungiyar, ta ɗauki matakin ne bayan da Kamfanin Man Fetur na Ƙasar (NNPC) ya miƙa mata nasa sabon farashin.
Shugaban ƙungiyar reshen Arewa, Bashir Ɗanmalan wanda ya tabbatar wa BBC da ƙarin, ya ce yanzu farashin zai kama ne daga naira 500 zuwa 600, dangane da yankin ƙasar.
Dama dai farashin man fetur ya tashi a sassa daban-daban na ƙasar tun bayan furucin sabon shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinu, wanda ya ce “Tallafin man fetur ya tafi.”
An rinƙa samun dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai, inda farashin lita ya rinƙa tashi babu ƙaƙautawa.