Kano Ayau Hausa, Labarai

Kamfanin MTN zai bude banki a Najeriya

Kamfanin sadarwa na MTN Nigeria ya sami amincewar hukumomin Najeriya domin ya bude banki, kamar yadda kamfanin ya sanar ranar Litinin.

MTN ya ce “Babban bankin Najeriya ne zai sanar da ranar da aka amince mu fara aiki, kamar yadda doka ta samar.”

Kamfanin ya ce sunan sabon bankin nasa MoMo Payment Service Bank Limited.

Kamfanin sai da ya jira amincewar na tsawon shekara biyu kafin aka amince ma sa ta hanyar ba shi lasisi kamar yadda BBC ta ruwaito.

A watan Nuwamba aka ba MTN Nigeria tare da Airtel Africa amincewa ta wucin gadi domin su bude bankuna, inda suke sa ran jawon hakulan ‘yan Najeriya kimanin miliyan 38 da ba su da asusun ajiyar banki a kasar.

Leave a Reply