BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Kamfanin BUA ya mayar da farashin siminti Naira 3,500

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, za’a na saida siminti a naira 3,500 kacal, a maimakon naira 5,000 zuwa 5,500 da yake a da.

Sabon farashin zai fara aiki a gobe Litinin, 2 ga watan Oktoba, 2023.

Kwanakin baya dai shugaban kamfanin na BUA, Abdussamad Rabiu yasha alwashin rage farashin siminti da zarar sun kammala gina sabon kamfaninsu na siminti a farkon shekara ta 2024.

Sai dai kamfanin yace yayi hanzarin cika alkawari ne saboda bawa jama’a daman more farashi mai rahusa tun kafun shekara ta 2024.

Shin ko sauran kamfanonin siminti irin su Dangote Cement zasu bi sahun BUA?

Leave a Reply