Daga Farfesa Umar Labdo Muhammad
Jiya muka tashi da labarin kama Malam Tukur Mamu, fitaccen dan jarida kuma wanda ya taimaka wajen kubutar da mutanen da yan fashin daji suka yi garkuwa da su bayan hari da suka kai a kan jirgin kasa mai zitga-zirga tsakanin Kaduna da Abuja. An kama shi tare da iyalinsa a birnin Kahira na kasar Misira a kan hanyarsu ta zuwa Umara.
Jami’an tsaron Nijeriya, wadanda suka samu taimakon yan sandan kasar Misira wajen aukar da kamun, sun ce dalilin kamun shi ne zarginsa da alaka da yan ta’adda kuma da amfana daga kudin fansa da suka yi zargin cewa shi ne ya rika karba daga hannun dangin wadanda aka yi garkuwar da su yana kai wa yan ta’addar.
Maganar da ake yanzu an tuso keyar Malam Mamu daga kasar Misira zuwa gida Nijeriya kuma yana hannun jami’an tsaro na DSS.
Akwai tambayoyi da dama da ya kamata a nemi amsarsu dangane da wannan al’amari.
Me ya sa ba’a kama mau a Nijeriya ba sai da aka bari ya fita zuwa kasar waje? Shin a boye yake, an neme shi an yasa sai da ya sauka kasar Misira aka ankara da inda yake?
Mamu dai ba a boye yake ba a sanda ya bar Nijeriya. Ba sulalewa ya yi ba, a gaban jami’an tsaron kasar nan ya fita bayan an buga hatimi a kan fasfonsa. Don me ba’a kama shi a filin tashin jiragen sama ba, ga misali, sai bayan da ya fita aka bi shi aka kama shi a kasar waje?
Shin anya wannan ba wata badakala ba ce aka shirya ta daura wa Mamu jakar tsabar ta’addanci domin kajin kasashen waje su bi shi su tsattsaga, irin yadda aka kullawa gwarzon dan sanda Abba Kyari?
Kuma jami’an tsaron Nijeriya ba su yi azanci ba a yayin da suka kama shi a kasar da ba ta da alkadari a tsakanin kasashen duniya, kasar da babu yanci a cikinta, kasar da mahukuntanta suke amfani da yansandansu wajen kashe yan kasa.
Don me za’a bi Mamu a kama shi a kasar waje, alhalin akwai halin kama shi a cikin gida tunda ba buya ya yi ba? Ana ma iya gayyatar sa kuma ya amsa gayyar tunda barayi ma a Nijeriya yan sanda (na EFCC) na gayyatar su kuma su amsa?
Yanzu dai-dai ne dan kishin kasa kamar Malam Tukur Mamu wanda ya sadaukar da rayuwarsa don ceto yan kasar da gwamnatinsu ta basar da su, a yi masa kamu irin wanda aka yi wa dan ta’adda Nnamdi Kanu wanda yake gaba da kasar Nijeriya kuma mabiyansa suna aikata ta’addanci a kan gwangwani da al’umma?
Kuma idan batun kamu ake don me ba’a kama manyan jami’an ma’aikatar jiragen kasa ta Nijeriya ba (NRC) wadanda sakaci da aikinsu tun farko shi ya kawo afkuwar ta’addancin da ya janyo garkuwa da mutane?
Wadan nan jami’ai sun samu rahoton sirri da yake tabbatar da yiwuwar kai hari kan jiragen dake zitga-zirga tsakanin Kaduna da Abuja amma suka yi banza da gargadin. Kuma an ba su shawara su soke tafiyar jiragen ta dare amma suka yi ko in kula? Babu shakka wadan nan jami’ai suna dauke da sashin alhaki na rashin rayuka da asarar dukiyoyi sakamakon wannan mummunan hari na ta’addaci.
Shin ba wadan nan ya kamata a kama ba? A iya sanina ba’a kama dayansu ba ko a gurfanar da shi a gaban kotu saboda sakaci da aiki.
Kowa ya san gazawar gwamnati da jami’an tsaronta wajen ceto wadan nan miskinai da aka yi garkuwa da su, maza da mata da yara, kusan tsawon wata shida (har yau akwai ragowar wadanda ba’a sako ba). Haka nan duniya ta ga rawar da gwarzo Tukur Mamu ya taka, da yadda ya yi amfani da martabarsa da martabar mai gidansa, Dr. Ahmad Gumi, ya jagoranci shiga tsakanin yan ta’addar da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su, inda ya samu nasarar ceto yawancinsu, a lokacin da gwamnati ta kasa katabus, sai rawar yan mata da zancen yan sanda.
Shin wannan kamu da aka yi wa Mamu mai cike da dirama ba nade tabarmar kunya a cikinsa? Anya ba borin kunya jami’an tsaron suke yi ba?
A karshen taronsu na Majalisar Zartaswa ta Tarayya (Fadaral Executive Council) da suke yi ko wace Laraba, Ministan Yada Labarai Lai Muhammad, ya fada wa manema labarai cewa babu masaniyar gwamnatin Tarayya dangane da wannan kamu. Shin wannan ba ya nufin watakila wasu yan tamore ne suke huce fushi da son nunawa Tukur Mamu iyakarsa don kada wani a nan gaba ya samu karfin guiwar shiga inda jami’an tsaro yan barazana suka kasa shiga?
Wasu jaridun kasar nan sun ayyana cewa ana zargin Malam Tukur Mamu da yin kashi-mu-raba shi da yan ta’addar na kudin fansa, inda suka zarge shi da kauwame Naira biliyan biyu a matsayin nasa kaso. Sai dai wani daga iyalan wadanda aka yi garkuwa da su din ya bayyana cewa Tukur Mamu bai shiga harkar karbar kudin fansa da mika su ga yan ta’addar ba, su iyalan ne ke kaiwa da kansu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito a fitarta ta yau Alhamis 8 ga watan Satumba. Don haka mene ne karfin wancan zargi, ko rauninsa, idan muka dubi shaidar shi mai wannan magana wanda, kamar yadda jaridar ta ce, ya nemi a sakaya sunansa (watakila saboda tsoron jami’an tsaro)?
Ala kulli halin, wannan kamu da jami’an tsaro suka yi wa Malam Tukur Mamu, a irin wannan yanayi, kuma a dai-dai wannan lokaci da ba’a gama warware matsalar ba (har yau da ragowar wadanda ba’a i da sako su ba kuma danginsu na tsoron kada hakan ya kawo cikas a kokarin yanto su), yana tado da tambayoyi wadanda wasu a cikinsu ba za mu so mu yi su ba saboda dabi’ar maudu’in ta tsaron kasa kuma da yadda ta shafi rayukan mutane wadanda har yanzu ba’a kubutar da su ba.
Fatanmu kawai shi ne a gudanar da al’amura a bude, kada a fake da maganar tsaro a yi wata kumbiya-kumbiya, musammam ganin yadda jami’an tsaro suka kutsa gidan Tukur Mamu a jiya da tsakar dare da sunan bincike, inda suka yi awon gaba da wasu kayayyaki mallakar mai gidan, bayan sun tilastawa wani yaron gidan ya sa hannu a kan wata takarda da ba’a bar shi ya karanta abinda ta kunsa ba.
Farfesa Umar Labdo Muhammad ne ya wallafa wannan rubutu a shafinsa na Instagram