Dan takarar gwamnan Kano na jam’iyyar ADC a zaɓen shekarar 2023, Sheikh Malam Ibrahim Khalil, ya shawarci zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da kada ya sake ya bari wasu gurbatattun ƴan siyasa su ziga shi ya yi rigima da mai gidansa, Rabi’u Musa Kwankwaso.
Sheikh Khalil, wanda ya zo na huɗu a zaɓen gwamna da a ka yi ranar Asabar, ya bada wannan shawara ne a wani shiri a Freedom Radio a Kano a jiya Talata.
A cewar Sheikh Khalil, Abba Kabir Yusuf ya maida hankali wajen toshe duk wata kofa da za a a iya amfani da ita wajen haddasa rigima tsakanin sa da Kwankwaso.
Ya kara da cewa a matsayin sa na ɗan sarauta, wanda kakanninsa suka yi shura wajen hakuri da dattaku, to ya daure ya gaji wannan halin ya yi hakuri da mai gidansa Kwankwaso da yan Kwankwasiyya, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta rawaito.
Ya kuma shawarci Abba da ya sani cewa al’ummar Kano zai mulka ba ƴan Kwankwasiyya ba, inda ya shawarci zaɓaɓɓen gwamnan da ya yi kokari sosai wajen cika alkawuran da ya ɗauka wa mutane a jihar.
“Kada Abba ya bari a ziga shi ya yi rigima da Kwankwaso. A matsayin sa na ɗan sarauta, wadanda aka sani da sun gaji hakuri, to ya daure ya yi hakuri tsakaninsa da mai gidansa da kuma yan Kwankwasiyya. Sannan ya toshe kunnen sa ga sauran al’ummar jihar tunda dama mulki ya gaji yabo da suka.
“Abu na biyu shine, Abba ya yi kokari ya zamana cewa gwamnatin sa gwamnati ce ta al’ummar jihar Kano ba gwamnatin ƴan Kwankwasiyya ba,” in ji Sheikh Khalil