Kano Ayau Hausa, Labarai

Jirgin sama dauke da mutum 132 ya yi hatsari

Wani jirgin saman China Eastern Airlines dauke da mutum 132 ya yi hatsari a lardin Guangxi, a cewar kafar watsa labaran kasar.

Kawo yanzu ba a san adadin mutanen da suka mutu ba.

Faduwar jirgin saman, kirar Boeing 737-800, a yanki mai cike da tsaunuka, ta haddasa tashin wuta a dajin da lamarin ya faru, a cewar kafar watsa labaran kasar.

Akwai fasinjoji 123 da ma’aikatan jirgi tara a cikin sa, a cewar hukumar kula da safarar jiragen sama ta China.

Jirgin mai lamba Flight MU5735 ya bar Kunming da misalin karfe daya da rabi na rana a agogon kasar a kan hanyarsa ta zuwa Guangzhou.

Kafar watsa labarai ta CCTV ta rawaito cewa an tura masu aikin ceto zuwa yankin da lamarin ya faru.

China ta kwashe tsawon lokaci ba ta samu matsalar hatsarin jiragen sama ba, kamar muka kalato daga BBC.

Babban hatsarin jirgin sama na karshe a kasar ya faru ne a watan Agustan 2010, lokacin da wani jirgin sama da ya taso daga Harbin ya yi hatsari a yankin Yichun inda mutum 42 suka mutu.

Jirgin saman ya fadi ne a kusa da yankin Teng da ke lardin Wuzhou. Guangxi shi ne lardin kudanci da ke makwabtaka da Guangzhou, babban birnin da ke kudu maso gabashin kasar.

Shafukan intanet da ke bin diddigin tafiye-tafiyen jiragen sama sun rawaito cewa jirgin saman bai fi awa daya da tashi ba, kuma yana dab da isa wurin da zai je.

A cewar shafin FlightRadar24, bayanai na baya-baya da suka samu game da jirgin saman sun nun cewa ya fadi da misalin karfe biyu da minti 22 na rana, inda yake nisan kafa 3,225.

One comment on “Jirgin sama dauke da mutum 132 ya yi hatsari

Leave a Reply