BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja zai dawo aiki

Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa ta shirya tsaf domin ta dawo da sufurin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna cikin wannan wata na Nuwamba.

Ministan sufuri na kasar Mu’azu Sambo ne ya bayyana haka ranar Litinin a Abuja babban birnin kasar, yayin bayyana ayyukan da ma’aikatarsa ta yi

Ya ce an shirya jami’an tsaro domin tabbatar da tsaron lafiyar fasinjoji , to sai bai bayyana takamaiman ranar da za a fara jigilar ba.

Ministan ya ce hukumarsa ta koyi darussa daga harin da aka kai wa jirgin kasa a watan Maris, lamarin da ya sa aka dakatar da sufurin jiragen kasa tsakanin manyan biranen biyu.

Haka kuma ministan ya ce an yi wani tsari da zai rika lura da zirga-zirgar jiragen kasan da kuma titin jirgin.

Ya kara da cewa tsarin zai bai wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da ma’aikatu da hukumomin gwamnati da jami’an tsaro damar ganin abun da ke wakana a kan titin jirgin ba tare da bata lokaci ba, kamar yadda muka kalato daga BBC.

Leave a Reply