A ci gaba da fafatawa a gasar rukunin Firimiya na Ingila (EPL), jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a fafata wasa mai zafi a tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Liberpool da takwararta ta Manchester City.
Wasan zai gudana ne a filin wasa na Liberpool da ake kira Anfield da misalin karfe 4 da rabi na yamma agogon Najeriya.
Kawo yanzu Manchester City ce take saman teburin gasar da maki 19 a wasanni bakwai sai kuma Liberpool ke matsayi na biyu ita ma da maki 19 amma suna da bambancin kwallaye.
Kamar yadda masana harkar kwallo suka yi hasashe, wannan wasa shi zai ba kowace kungiya damar ci gaba da jan ragamar gasar idan ta samu nasara. Sannan duk kungiyar da ta yi sake aka doke ta a wasan, to akwai yiwuwar a yi mata fintinkau, ganin yadda sauran kungiyoyin da ke biye suke kokarin tsere wa tsara.
Tun bayan da aka fara gasar kawo yanzu, dukan kungiyoyin biyu, wato Liberpool da Manchester City ba su samu rashin nasara ba, sai dai kunnen doki da suka yi a wasa dai-dai.
Idan za a tuna a kakar wasan bara, kulob din Manchester City ne ya zama zakara a gasar ta Firimiya. Kulob din Liberpool bai taba lashe wannan kofi ba tun bayan da aka canja wa gasar suna zuwa Firimiya a shekarar 2000 kimanin shekara 18 da suka wuce.
Tuni magoya bayan kungiyoyin biyu suka fara hasashen kungiyar da za ta samu nasara a wasan, kamar yadda ake ganin gidajen kallon kwallon kafa za su cika makil don ganin yadda wasan zai kaya.