Jarumar masana’antar fina-finai ta Kannywood, Nafisa Ishaq, ta roƙi Sheikh Aminu Daurawa da ya yafe mata a kan fefen bidiyo da ta yi ta gaggaya masa magana ta kafar tiktok.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a wani karatu da ya yi ta yawo a kafafen sadarwa a kwanan nan, an jiyo Sheikh Daura na cewa al’aurar mace ba guri ba ne mai kyawun gani tunda ta nan ma najasa ke fita.
Wannan karatu, da jama’a da dama, musamman mata su ka yi wa mummunar fahimta, ya janyo cecekuce a kafafen sadarwa a tsakanin mata.
Da ga cikin matan da su ka riƙa maida martani ga Sheikh Daurawa har da Nafisa, wacce ta yi faifen bidiyo ta na maida wa Mallam martani.
Sai dai kuma da ga bisani, jarumar ta nuna nadamar ta a wani faifen rediyo, ta na baiwa Mallam Daurawa haƙuri.
Da ga nan ne kuma, sai Nafisa ta kuma yin faifen bidiyo ta na sake bada hakuri, inda ta ce “sharrin shaiɗan ne”.
“Ina mai ƙara baiwa Mallam hakuri da kuma sauran ƴan uwa Musulmi baki daya. Na yi kuskure. Ba wai na faɗa don batanci ga Mallam ba. Na yi kuskure kuma na yi nadama.
“Na yi audio na bada hakuri, amma na ga kamar bai gamsar da jama’a ba, shi ya sa na yi bidiyo domin sake bada hakuri. Dan Allah Mallam ka yafe mini. Al’ummar Musulmi kuma ku yafe mini,” in ji Nafisa.