Al’ajabi, Kano Ayau Hausa

Hotuna: ‘Yan majalisar Shura ta Shekarau suna raba kudin ‘tallafin’ Atiku

Wasu hotuna sun nuna wasu mambobin Shura, majalisar shawara ta harkar siyasar Sanata Ibrahim Shekarau, suna raba wani kaso na Naira miliyan 100 da ake zargin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya bayar domin tara magoya bayan jam’iyyar a ziyarar da ya kai Kano.
Wasu majiyoyi sun shaidawa DAILY NIGERIAN cewa ɗan takarar shugaban ƙasa ya yiwa shugabannin PDP na Kano wanka da kuɗi har naira miliyan 130, inda Malam Shekarau ya samu kaso mafi tsoka na Naira miliyan 100, shi kuma ɓangaren Aminu Wali ya samu Naira miliyan 30.
Sai dai wata majiyar ta ce kudin na tallafi da Atiku ya ba wadanda ambaliya ta shafa a Kano
A karshen watan Agusta ke dai Atiku ya ziyarci Kano domin karɓar Malam Shekarau, wanda ya sauya sheƙa daga jam’iyyar NNPP ta Rabiu Kwankwaso zuwa PDP.

Leave a Reply