Kano Ayau Hausa, Manyan Labarai

Hisbah ta kama mata masu zaman kansu a Kano kafin Ramadan

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama mata da dama masu zaman kansu a wani mataki na tsabtace jihar kafin Azumin Ramadan.

Hukumar ta kai samame ne a gidajen da ake tara mata masu zaman kansu a birnin Kano da wasu kananan hukumomi.

Babban daraktan a hukumar ta Hisba a Kano Mallam Abba Sufi, ya shaida wa BBC cewa sun kama Mata masu zaman kansu guda 26 a garin Kano kawai kuma har an gurfanar da wasu daga cikinsu a gaban kotu.

“Kotu ta yanke wa wasu hukuncin daurin shekara daya karkashin dokar hana karuwanci,” in ji shi kamar yadda BBC ya ruwaito shi tana fada.

Ya kuma ce sun sun kai samamen a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Tambarawa da suka yi suna wajen tara mata masu zaman kansu.

A Dawakin Kudu hukumar ta ce ta kama mata da dama amma ta yi yarjejeniya da su, inda suka amince su fice daga jihar da ke aiwatar da shari’ar musulunci.

Hisbah a Kano ta kai samamen ne yayin da ya rage ‘yan kwanaki a fara gudanar da azumin watan Ramadana.

Malam Sufi ya ce Kano jiha ce ta addinin musulunci wacce take shari’ar musulunci, kan haka ne kuma hukumar Hisbah ta kaddamar da samamn a wuraren da ake zargi na mata masu zaman kansu ne da wuraren da ake zargi ana ayyukan masha’a.

Ya ce hukumarsu za ta ci gaba da samame a gidajen mata masu zaman kansu domin tsabtace jihar a lokacin watan Ramadan inda ya yi kira ga jama’a su sanar da hukumar gidajen da suka san ana aikata ayyukan masha’a.

Leave a Reply