BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Hatsarin mota ya ci mutum 30 a hanyar Kano

Kimanin mutane talatin ne suka rasu, tare da jikkatar goma sha biyu, a wani hatsarin mota da ya afku a hanyar Kano zuwa Zaria.

Babban jami’in hukumar kiyaye afkuwar haɗura ta ƙasa FRSC shiyyar Zaria, ACC Abdurrahman Yakasai ne ya tabbatar ga hakan ga Freedom Radio.

Ya ce, hatsarin ya afku ne da yammacin ranar, Alhamis a daidai garin Tashar Musa da ke ƙaramar hukumar Maƙarfi ta jihar Kaduna.

Motocin da hatsarin ya rutsa da su sun haɗar da Hummer Bos ƙirar Toyota mai ɗaukar mutane 18, da kuma wata motar Volkswagen saloon a cewarsa.

Leave a Reply