BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Harin jirgin ƙasa: Ƴan ta’adda sun saki ɗan gidan Ango Abdullahi

Sadiq Abdullahi, ɗan gidan Farfesa Ango Abdullahi, Jagoran Ƙungiyar Dattawan Arewa, NEF l, ya shaƙi iskar ƴanci daga hannun ƴan bindigar da su ka kai hari kan jirgin ƙasar Abuja-Kaduna a ranar 28 ga watan Maris.

A jiya Litinin ne wani a dangin su Abdullahi ɗin ya ce tun ranar Juma’a ƴan bindigar su ka sake shi bayan ya shafe kwanaki 31 a hannun su.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa ƴan bindigar ne su ka gane cewa Sadiq ɗin ɗan gidan Ango Abdullahi ne shine su ka sasanta da mahaifan sa.

“Ka san sasanta wa ta yi nisa tsakanin gwamnati da ƴan bindigar kuma ba ma so mu kawo matsala a haka. Amma dai ga dukkan alamu su ƴan bindigar sun fahimci ko wanensu Sadiq shi ya sa su ka sasanta da iyalin sa domin sakin sa,” in ji wata majiya da ta shida wa jaridar Daily Nigerian Hausa.

Har yanzu dai dangin Abdullahi ɗin ba su fitar da wata sanarwar a kan wannan lamarin ba.

Leave a Reply