Tsohon mashawarci ga Gwamnan Jihar Kano a kan harkokin yad5a labarai, Salihu Tanko Yakasai ya fice da ga jam’iyyar APC.
A yau Litinin ne dai Yakasai ya sanar da ficewar ta sa da ga jam’iyar a yayin taron manema labarai a Kano.
Ya ce ya ɗauki matakin barin jam’iya mai mulkin ne sabo da rashin cika alkawuran da ta yi wa al’ummar ƙasar nan.
Yakasai, wanda a ke yi wa lakabi da Dawisu, yace Jam’iyyar APC ta gaza sauke mafi yawa daga cikin nauye-nauyen data daukarwa ƴan Nijeriya, dama abubuwan da ya kamata a ce gwamnati ta yiwa al’ummar ta.
“Da ni a ka yi tallan jam’iyyar APC a dukkanin mafi yawa daga cikin jihohin Nijeriya , kuma mun yiwa al’ummar kasar nan alkawura. Amma ni da kaina na gamsu da cewa jam’iyyar ta gaza dauke alkawuran data yiwa yan kasa”. Inji Yakasai
Salihu Yakasai, wanda Gwamnatin Kano ta kora da ga mukaminsa saboda irin kalaman da yake yi na sukar gwamnatin tarayya, ya ce ya dade ya na fadawa gwamnatoci gaskiya tun lokaci da PDP ta ke kan mulki.
“Saboda irin matsalolin da ƴan ƙasar nan suke cikin na rashin tsaro, rashin baiwa yan kasa kyakykyawar rayuwa , sanya ƴan kasa cikin mawuyacin hali, da ma wasu matsalolin, shi ya sa na fice daga jam’iyyar APC a wannan rana”.inji Salihu Yakasai
Tanko Yakasai yace nan gaba kadan zai baiyana Inda zai koma domin cigaba da gwagwarmayar siyasa.
-Daily Nigerian