Ayyukan da suka yi fice musamman ma wadanda suka amfani al’umma da wasu suka yi ko Kamfanoni da kuma Hukumomin gwamnati , ko kuma kungiyoyi wadanda suna sa tubulin cigaban al’umma ne wadanda wasu ma zasu iya koyi da hakan, ba zai tafi hakanan ba. Dama shi aikin kirki haka yake ba ayin shi ya tafi hakanan. Leadership ta fara yin wannan gwarzon aiki shekareau da suka wuce, kamar dai yadda aka saba yi shekarun baya, wannan shekarar ma ta 2018 su gwarzayen da aka zaba an shirya hakan ne su mutanen wadanda suka kasance gwarzayenta.
Kafin dai a kai ga daukar mataki akan ko su wanene an yi waya, ga kuma wasiku, sai kuma bincike, da muhawara da kuma tafiye-tafiye. Ga kuma tarurruka wadanda su shugabannin wannan al’amarin gwarzayen shekara da suka yi, akan wadanda ya dace a zaba, to daga karshe dai an yanke shawara zabar wadannan mutanen a matsayin gwarzayen wannan shekara ta 2018.
Gwarazayen dai an raba sune daban- daban akwai masu kamfanonin dake zaman kansu, ga kuma gwamnoni, sai kuma wadanda suka shahara a siyasa da kuma Hukumomi, kai daga karshe ma har akwai kayayyakin da ake amfani dasu.
Alhaji Aliko Dangote
Gidauniyar Dangote wata hanya ce wadda shi shugaban Aliko Dangote ya kafa da kan shi, saboda ya cimma burin shi na a taimaka wa al’umma, shi ya sa ita gidauniyar ta maida hankalinta wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya wajen taimaka masu wajen yin wasu ayyuka. Ayyukan kuma wadanda zasu yi maganin yunwa da matsalolin da ake fuskanta na al’amarin ruwa. Ga kuma al’amarin daya shafi kiwon lafiya da kuma al’amarinn daya shafi ilimi da kuma taimakama wa al’umma saboda su gina kansu yadda wasu ma zasu zo su rabu da su, su tashi tsaye a garuruwan al’umma. Wannan ba wani abin mamaki bane saboda ya kasance na shida a duniya idana ana maganar daukaka al’umma.
A shekarar 2014 ya ba gidauniyar Naira bilyan 200 dalilin bada wannan kudin shineb saboda ita gidauniyar ta fara yin muhimman ayyukan da suka sa gaba. Bayan haka kuma an kafa wata Academy wadda makaranta ce inda za a koya ma matasa koyon sana’oi da kuma fasaha wadanda zasu yi aiki a kamfanonin Nijeriya. Hakanan ya bada gudunmawar Naira milyan 153 domin taiamakawa gwamanatinNijeriya wajen yakar kwayar cutar Ebola a shekarar 2014 da kuma dala milyan 3 wanda taimako ne ga kungiyar kasashen Afirka.
Wanna shekara ma gidauniyar ta Dangote ta kashe Naira bilyan 8, yawancin ayyukan sun hada da saboda manyan gobe wato yara ko kuma matasa, alal misali akwai Dangote Business School wadda take Kano an gina ta a jami’ar Bayero dake Kano akan kudi Naira bilyan 1.2, ita ce makaranta ta farko wadda Hukumar kula da jami’oi ta amince da ita. Hakanan ma ya gina makarantar sakandare ta Naira milyan 120 a Kudu maso yammacin Nijeriya karkashin kungiyar addini ta Nawar ad-deen. Hakanan ma ya gina School of Business ta Naira milyan300 a jami’ar Ibadan a shekarar 2016 lokacin da aka bas hi digirin girmamawa. Hakanan ma ya gina dakunann kwanan dalibai a jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya akan kudi Naira bilyan daya, hakanan ma ya zuba hannayen jari a jihar Niger, ya kuma raba Naira milyan 250 ga mutane 25,000, an zabi mata 1,000 daga cikin kananan Hukumomi na jihar 25. Jihar Nasarawa ma ba a barta baya ba, saboda an raba Naira milyan 130 ga ‘yan asalin jihar da kuma matasa 13,000, sai kuma mata 1,000 wadanda aka zabo daga kananan Hukumomi 13 na jihar. Sai kuma jihar Borno inda ya bayar da Naira bilyan 2 saboda a sake gyara wuraren da suka lalace a sanadiyar annobar Boko Haram, sai kuma kayayyakin gini na Naira bilya daya saboda gina gidaje 200 a kauyen Dangote wanda ke Dalori Maiduguri, bayan ma akan maganar dakunan ita gidauniyar ta taimaka ma mata da Naira 100,000 ko wacce, waya, da kuma ATM sai kuma asusun ajiya, gidauniyar Aliko Dangote ta taimaka wajen kudaden aikin makarantar da aka gina, a wurin da gidaje 200 su ke. Sai kuma bangaren tsaro gidauniyar ta bayar da gudunwar motoci 150 ga rundunar ‘yansanda ta kasa, kudaden motocin sun kai bilyoyin Naira, si kuma taimakon kasa da kasa na harkar ilimi inda gidauniyar ta bayar da taimakon dala 60,000,. sai kuma cibiyar muradun cigaba na nahiyar Afirka da dala 500,000.
Idan kuma aka dawo gida gidauniyar an taimaka ma James College Agbor cikin jihar Delta da milyan 20 saboda ta yi amfani da kudaden wajen ba dalibai ‘yan asalin jihar samun damar karo ilimi. Sai kuma lokacin Azumin watan Ramadan ya taimaka ma jihohi 36 da kuma babban birni tarayya Abuja da kayayyakin abinci , abinda yake kashe Naira milyan 700 ko wacce shekara.
Imam Abdullahi Abubakar
Shi dai wannan Limami mai shekaru 83 yana zaune ne a kauyen Yelwa Gindin Akwati a gundumar Gashish ta karamar Hukumar Barikin Ladi ta jihar Plateau.
Lokacin da aka faye yin rikice -rikice a jihar cikin watan Yuni 24 na wannan shekara ta 2018, an dai kai ma garin harii inda aka kashe mutane fiye da 200, wajen karfe uku da rabi na dare kafin a fara sallar La’asar si mutane 300 wadanda duk kiristoci ne, babu zato ba tsammani sai suka samu kansu a garin Yelwa Gindin Akwati, su dai sun kasa gudu shi yasa hakan ta faru.
Honorabul Ifeanyi Ugwuanyi Gwamnan Jihar Enugu
Shi dama babban al’amarin daya damu da shi shine jin dadin marasa karfi daga cikin al’umma wato wadanda basu da yadda au iya tafiyar da kansul, kfin dai ya ci zaben gwamnan jihar yawancin hanyoyi na jihar suna cikin wni halin da baa iya cewa komai.
Ya fara da aiwatar da wasu ayyukan kawo ci gaba gyara da kuma yin wasu sababbin hanyoyi da kuma ayyuka a 9 mile, Nsukka Abakpa da kuma Emene, hkanan kamar dai yadda shi tsarin ci gaba na gwamnan yake, ya kammala wasu ayyukan ci gaba 35 a cikin kananan Hukumomi 17 na jihar. Cikin shekaru uku na mulkin shi ya kashe bilyoyin Naira wajen gina hanyoyi da kuma gyaran wasu, a sassa daban daban na jihar wanda ya kai fiye da kilomita 300. Sai kumja ta bangaren tsaro nan ma ya taka muhimm,iyar rawa saboda kumwa akwai wadanda suka yi tsammanin shi zaman lafiya ya danganta ne akan yadda yake tafiyar da jihar. Saboda akwai hadin kai da kuma fahimtar juna shi da jami’an tsaro na jihar.
Alhaji Yahaya Adoza Bello Gwmann Jihar Kogi
Bayan daya samu sa’ar kwato jihar daga hannun wadanda suke ganin duk yadda suka dama zasu iya yi da jihar, gwamnan ya fara da samun abubuwan da zai yi aiki dasu wajen fara tunkarar al’amarin rashin tsaro wanda ya addabi ita jihar. Gwamnatin jihar ta sawo motoci fiye da 200 da kuma mashina 500 wadanda ya rarraba ma jami’an tsaro daban daban a fadin jihar. Ya fara da al’amarin yin bincike na ma’aikatan jihar saboda ya gano ma’aikatan da ba na gaskiya ba. Saboda gwamantin jihar tana kashee kudade masu yawa saboda biyan albashi. Wannan tsarin kuma yayi kyau saboda kuwa n gano su.
Ta banagren aikin gona ya sayo taraktocin noma 375 da kuma duk wasu kayayyakin da ake amfani dasu saboda bunkasa aikin gona,
Gwamna Dabe Umahi na Jihar Ebonyi
Gwaman jihar Ebonyi Injiniya Nweze Umaihi ya fara al’amuran shi a jihar da farar saka, saboda a kasancewar shi na wanda ke jan ragamar mulkin jihar a kusan shekaru hudu, ya canza alkiblar ita jihar daga kauye zuwa wata babbar alkarya , musamman ma ta bangaren aikin gona da kuma abubuwan more rayuwa.
Zuwa yanzu nasarorin da gwamnati Umaihi ta cimmawa swuna karab ma shi farin jini, daga kusa da kuma nesa, saboda lokacin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kai ziyara ajihar, ya kaddamar da wasu daga cikin ayyukan da shi gwamnan ya yi, wadanda sune suka sa ake cewar ya samu ci gaba.
Darius Ishaku Gwamnan Jihar Taraba
Darus Dickson Ishaku ya gaji jihar ne lokacin da bata da abubuwan more rayuwa, ga kuma rashin kudade, ssai kuma fadace-fadace na kabilanci wanda yayi kokarin durkusar da jihar, wasu daga cikin cigaban daya samu sun hada da duk d ayake ya gaji al’amari na yawan yamutsin kabilanci amma yanzu jihar ta fara samun zaman lafiya tsakanin al’umma.
Idann kuma aka duba ta bangren samar da abubuwan more rayuwa , wutar lantarki na daya daga cikin su domin kuwa ya kaddamar da tiransifoma a kauyuka 85 inda yanzu ya hada su da tashar wutar lantarki ta kasa a karkashi babbab garin Kini, cikin karamar Hukumar Lau ta jihar.
Sanata Bola Ahmed Tinubu
Shi tsohon gwamnan jihar Lagos ne kuma tsohon Sanata, babban jagora a jam’iyyar APC, kuma jigon siyasa yanzu a sashen Kudu maso yamma, ko shakka babu yanzu tauraruwar shi tana cikin haske ba ma a sashen Kudu maso yamma ba, kusan duk illahirin Nijeriya.
A shekarar 2017 lokacin da yake wa’adin shin a biyu a matsayin gwaman jihar Lagos, mutane ba zasu manta da takin sakar data kasance ba tsakanin shi da tsohion shugaban kasa Olusegun Obasanjo, saboda gwamantin tarayya ta rike masu kudadensu na watanni da suka wuce hudu, haka kuma jihar ta tafi, abin sai da aka je kotu, lokaci matamakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo shine kwamishinan shari’a kuma Attone janar na jihar. Amma daga karshe gwamnatin ta samu nasara akan gwamnatin tarayya, wanda ya tsaya lokacin shari’ar har aka kai ga samun nasara a matsayin shi na lauya.
Sanata Bukola Saraki
Sanata Bukola Saraki shine Shugaban majalisar dattawa ta kasa ko shakka babu shine daga cikin Shugabanni majalisar dattawa, wanda har maganar yadda aka zabe shi ma shugaban, har zuwa yanzu tana cigaba da daure ma wasu kai na yadda duk al’amarin ya kasance.
Siyasa ku san shi Bukola Saraki ko an ce ma ya gajieta ba l;aifi aka yi ba, idan aka tuna da mahaifin shi marigayi Sanata Abubukar Sola Saraki, wanda shi ma yah au kan mukammin shugaban masu rinjayea a majalisar dattawa zamanin mulkin tsohon Shugaban kasa Shehu Usmana Aliyu Shagari lokacin jam huriya ta biyu a karkashin jam’iyyar NPN. Shi ba bako ne saboda kuwa ba haye yayi ba gado ne ya yi watakila ma shi yasa duk wani zafin daya ke dauka ko kuma shiga, abin kamar baya damun shi. Idan aka ui la’akari da yadda aka yi ta kai gwauro da mari wajen halartar shari’un daya ke fuskanta.
Farfesa Is-hak Oloyede sabon shugaban Hukumar JAMB
Hukumar shirya jarabawar shiga jami’oi da kuma manyan makarantu ta kasa, ita Hukuma ce wadda aka sani cewar ta sha shiga cikin manja dangane da harkokin da suka shafi karbar rashawa da kuma cin hanci. Wani ala’amari kuma sai kuma ga shi duk daia a karkashi Hukumar sai aka fara samun canji akan kudaden shiga asanadiyar zuwan shi sabon rajistara,., wanda abin ya fara ne daga milyan uku, har dai abin ya kai ga an samu Naira bilyan biyar, wannan kuma duk abin ya faru ne cikin shekara daya.
Thomas Etuh
Shi shugabane kuma babban jami’i na kamafani mai zaman kan shi wanda ake kira TAK Continental, ya taka muhimmiyar rawar wajen tsarin takin zamani na Shugaban kasa Muhammadu Buhari. Shi shugaba ne na kungiyar masu yin takin zamani.
Kamfanin Airtel
Kamar dain yadda kowa ya sani shi kamfani Airtel kamfani ne na wayar tafi da gidan ka, wanda shi ma yana bada dama ne ga masu amfani da network na shi, wajen tafiyar da harkokin sun a sadarwa.
Airtel a matsayin shin a kamafanin da yake batar da dama ta sadarwa, yanzu yana bayar da ita damar, a cikin fiye da manyan birane da kuma garuruwa fiye da sittin a jihohin Nijeriya. Yanzu haka kuma yana da karfin samar da dama ta shiga kafar sadarwa ta internet na layin 4 G.