Kano Ayau Hausa, Manyan Labarai

Gwamnatin Kano ta haramta zanga-zanga

Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya haramta duk wata zanga-zanga a bainar jama’a, Sannan yabada umarnin kama wasu dalibai da ake zargin sun yi zanga-zanga

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanya takunkumi mai tsauri akan duk wani taron jama’a da akeyi da niyyar gudanar da zanga-zanga a jihar, tare da yin amfani da ikon da aka bashi a matsayinsa na babban jami’in tsaro na jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Laraba 29/5/2024.

Bisa ga matsayinsa, na gwamna ya umurci ‘yan sanda, da hukumar tsaro ta farin kaya, da hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya, da su kamo, tare da tsare, da gurfanar da duk wani mutum ko kungiya da ke gudanar da zanga-zanga a kan titunan Kano.

Wannan ƙwaƙƙwaran mataki anyi shine da nufin kawar da duk wata yuwuwar tabarbarewar doka da oda da maƙiyan jihar suka shirya.

Mun samu sahihan bayanan sirri da ke nuni da cewa wasu jiga-jigan jam’iyyar adawa a Kano sun tsara shirin daukar nauyin kungiyoyin dalibai da masu fafutukar siyasa daga wasu jihohin Arewa maso Yamma domin tada hargitsi a fake da cewa suna goyon bayan tsige tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero.

Gwamnatin jihar ta fito karara ta haramta zanga-zanga ko jerin gwano akan tituna ko wace iri ce, kuma za a kama mutanen da aka samu a kan titunan Kano suna yin irin wadannan ayyuka nan take.

Tacikin wannan sanarwar, muna gargadin kungiyoyin dalibai da su guji yin amfani da masu tayar da rikici a jahar kano.

Gwamnan ya bukaci daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum domin jihar ta ci gaba da zaman lafiya, kuma gwamnati za ta ci gaba da sanya ido kan lamarin don gaggauta magance duk wani mutum ko kungiyar da ke kokarin kawo cikas ga zaman lafiya da jihar ke samu a halin yanzu.

Leave a Reply