Kano Ayau Hausa, Labarai

Gwamnati ta dakatar da jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja

Biyo bayan harin da ‘yan ta’adda suka kai a wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja a daren Litinin, Hukumar Jiragen Kasa, NRC ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jirgin na wani dan lokaci.
A sanarwar da hukumar ta fitar a twitter, ta ce, “zuwa ga fasinjojinmu, mun dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa a hanyar Kaduna zuwa Abuja na wani dan lokaci.
“Za mu sanar da mataki na gaba na gaba kadan.”

Leave a Reply