Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya dira a asibitin Murtala, babu zato ba tsammani.
Gwamnan wanda ya isa asibitin na Murtala a safiyar yau, ya zazzagaya asibitin, inda ya duba marasa lafiya sannan kuma ya ganewa idonsa halin da asibitin yake ciki.
Haka kuma gwamna ya tattauna da wasu manyan jami’an asibitin, inda ya ƙara tabbatar musu da aniyar gwamnatinsa na ta inganta harkokin lafiya a jihar Kano.
Daga Asibitin Murtala, Gwamnan ya kai ziyarar Tashar Ruwan Sha na Chalawa, inda ya gane wa idona halin da wajen yake.