WASANNI

Guragu suna neman tallafi don tafiya gasar cin Kofin Duniya

Kungiyar kwallon kafa ta guragu ta Najeriya tana neman tallafi daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu da kuma daidaikun mutane don ganin an tallafa musu sun halarci gasar cin Kofin Kwallon Kafa ta Guragu ta Duniya da za a yi bana a kasar Meziko.

Daya daga cikin ’yan kwallon guragun da yake buga wa kulob din guragu na Arsenal da ke Ingila Micheal Ishiguzo ne ya yi wannan kira a shafin sadarwarsa na yanar gizo a shekaranjiya Laraba jim kadan bayan ya tattauna da gidan rediyon BBC, Landan.

Dan kwallon guragun ya yi kiran ne a madadin Kungiyar Kwallon Guragu ta Najeriya.  Ya ce saboda rashin kulawar da Ma’aikatar Matasa da Wasanni da kuma Gwamnatin Tarayya ke yi musu ne ya sa suka kasa halartar gasar cin kofin kwallon kafa na guragu na duniya sau uku a jere.

Ya ce ganin gasar ta sake karatowa da za a gudanar a kasar Meziko kafin karshen bana ce ya sa suka sake yunkurin neman tallafi don ganin sun halarci gasar.

“Ina mamakin yadda Ma’aikatar Matasa da Wasanni ta Najeriya take yi mana rikon sakainar kashi duk da irin gudunmawar da muke bayarwa a bangaren wasan kwallon kafa a ciki da wajen kasar nan.  Ina ganin suna yin haka ne ganin mu nakasassu ne. Mun kasa halartar gasar sau uku a jere saboda rashin tallafi, don haka muka yanke shawarar mu halarci gasar a wannan karo,” inji shi.

Micheal Ishiguzo ya  ce tuni a madadin kungiyar suka bude asusun neman tallafi a yanar gizo inda suke sa ran tara kimanin Dala dubu 68 (kimanin Naira miliyan 24 da dubu 480) don ganin sun halarci gasar, kuma yana sa ran za su samu tallafi nan ba da jimawa ba.

Taken asusun neman tallafin shi ne “GoFundMe,” kuma ya janyo hankalin mutane da dama a sassan duniya, rahotanni sun ce tuni asusun ya fara samun tallafi a Ingila.

Micheal Ishizugo ya ce yana da tabbacin idan suka halarci gasar cin Kofin Duniya na kwallon kafa ta guragu a Meziko za su ba marada kunya, kuma takwarorinsa da ke wasa a gida za su samu nasarar tafiya kasashen Turai don ci gaba da kwallo kamar yadda ya samu zuwa Ingila.

Leave a Reply