An tsinci gawar ɗan wasan Ghana Christian Atsu a ƙarƙashin ɓaraguzan gidansa, kamar yadda wakilin ɗan wasan ya bayyana, kusan makonni biyu bayan da girgizar ƙasa ta afka wa Turkiyya da Siriya.
Atsu mai shekarar 31 ya yi wasanni a ƙungiyoyin Chelsea da Newcastle.
Tun bayan girgizar ƙasar – da ta lalata gidaje da dama a birnin Hayat inda ɗan wasan ke zaune – ba a sake jin ɗuriyar ɗan wasan ba.
Tun da farko ƙungiyarsa ta bayyana cewa an kuɓutar da shi da munanan raunuka, to sai dai daga baya, wakilinsa ya tabbatar da cewa ba a ceto shi ba.
“Cikin mummunan tashin hankali da firgice, nake sanar da masu yi wa Atsu fatan alkairi cewa an gano gawarsa da safiyar yau,” kamar yadda wakilinsa Nana Sechere ya bayyana a shafinsa na Tuwita kamar yadda BBC ta ruwaito.
“Ina miƙa sakon ta’aziyyata ga iyalai da masoyansa. ina kuma so na yi amfani da wannan dama wajen mika godiya ga duka mutane game da addu’o’i da goyon bayan da suke ba shi”.