An samu faɗuwar farashin kayaki a Najeriya karon farko cikin wata 11 zuwa kashi 21.34
Farashin kayaki a Najeriya ya tashi sau wata 10 a jere har zuwa watan Nuwamban 2022, lokacin da ya kai kashi 21.47
Rahoton Hukumar Kididdiga ta Najeriya NBS, ya nuna cewa farashin kayaki ya ragu da kashi 0.13 tsakanin watannnin Nuwamba da Disamba.
Rahoton ya ce ” A watan Disamban 2022, an samu raguwar farashin kayaki zuwa kashi 21.34 idan aka kwatanta da Nuwamban 2022 din lokacin da farashin ya kai kashi 21.47,” kamar yadda BBC ta kalato.
Sai dai a tsawon shekarun nan, farashin kayaki yana kashi 5.72 idan aka kwatanta da hauhwarsa da aka samu a watan Disamban 2021, lokacin da yake kashi 15.63.
Hukumar ta ce hakan na nuna cewa an samu hauhawar farashin kayaki a watan Disamban 2022, idan aka kwatanta da watan a shekara ta 2021