Labarai

EFCC ta gurfanar da dan takarar gwamnan Kano a kotu

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta’annati, EFCC, ta gurfanar da dan takarar gwamnan jihar Kano da ke arewacin kasar gaban kuliya.

Sanarwar da mai magana da yawun EFCC, Tony Orilade, ya aike wa manema labarai ta ce ta gurfanar da Abdulsalam Saleh Abdulkareem, mutumin da ke yi wa jam’iyyar Green Party of Nigeria, GPN, takarar gwamna a wata babbar kotun jihar bisa zargin aikata laifi tara ciki har da damfara ta kudin da suka kai $1,320,000.

BBC ta ruwaito cewa an gurfanar da dan takarar gwamnan ne tare da Ebere Nzekwe, wanda ake zargin su da aikata laifukan tare, a kotun da mai shari’a Lewis Allagoa ke jagoranta.

Mutumin da ya kai su kara ya yi zargin cewa a shekarar 2014 mutanen biyu sun damfare shi ta hanyar karbar kudaden, wadanda suka ce za su rika juyawa domin yin kasuwancin da za a rika samun riba.

An yi zargin cewa Abdulsalam ya hadu da mai taimakawa wanda ya shigar da karar, mai suna Muhannat a wani otal da ke kasar Kuwait inda suka tattauna kan yadda za a karbi kudin.

Daga nan ne, a cewar EFCC, Abdulsalam ya gayyaci mutumin zuwa Najeriya inda a can ne ya karbi kudin.

Sai dai mutanen da ake zargin sun musanta aikata laifi lokacin da aka karanta musu laifukansu.

Mai shari’a Allagoa, ya bayar da belinsu a kan N100m da kuma mutumin da zai tsaya musu, wanda kuma dole ne ya mallaki gida a Kano.

An dage sauraren karar zuwa ranar 29 ga watan Janairu na 2019.

Leave a Reply