Kano Ayau Hausa, Siyasa

EFCC na neman dan takarar sanatan Kano ruwa a jallo

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta bayyana neman ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC mai mulki, AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura.

Lauyan hukumar EFCC, Ahmad Rogha ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Litinin bayan da aka dawo da batun shari’ar dala miliyan 1.3 da ake yi wa A.A Zaura a babbar kotun tarayya da ke Kano.

Duk da cewa shari’ar da aka shirya yi wa ɗan siyasar ba ta samu ba, saboda rashin halartar alkalin da ke sauraron shari’ar, wanda aka ce yana halartar wani taron ƙasa a wajen birnin na Kano.

Haka kuma lauyan na EFCC ya bayyana cewa ya kamata A.A Zaura ya kai kansa ga hukumar.

“Muna neman Zaura kuma za mu kama shi da zarar mun same shi”.

”A ƙa’ida, ya kamata a ce yana hannunmu domin kuwa kotu ta tabbatar da haka, amma ina tabbatar da cewa za a kama shi tare da gurfanar da shi a gaban kotu a zamanta na gaba ranar 30 ga Janairun 2023”.

Leave a Reply