BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Duk da hana zuwa Umara, Cutar Kurona ta bulla a Saudiyya

Saudiyya ta tabbatar da samun bullar cutar Coronavirus a karon farko a kasar a ranar Litinin.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya ambato Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyyan tana tabbatar da bullar cutar a jikin wani dan kasar da ya dawo daga Iran, kamar yadda BBC ua ruwaito.

Ma’aikatar Lafiyar ta ce mutumin bai bayyana cewa daga Iran ya dawo ba, inda ya shiga kasar ta tashar jirgin ruwa.

Ma’aikatar ta ce ”cikin matakan da muka dauka na kiyaye bazuwar cutar, mun tura jami’a na musamman domin duba wanda ya shigo da cutar, da kuma yi masa gwaji. Bayan gwajin da aka yi masa sai aka gano yana dauke da cutar”.

Ma’aikatar ta tabbatar da cewa wanda yake dauke da cutar an killace shi a asibiti.

Ta kuma bayyana cewa tuni aka nemo wadanda ya yi mu’amala da su kuma aka yi musu gwaji kuma idan sakamakon ya fito za a bayyana shi.

Ko a safiyar Litinin sai da ministan lafiya na kasar Tawfiq Al-Rabiah ya bayyana cewa kasar ta Saudiyya ba ta samu wani mai dauke da cutar ba bayan ta yi gwaji ga mutum 290 da ake zargi a baya.

Ministan ya bayyana cewa ”muna sa ido ga duk wani mai shiga kasar Saudiyya, musamman wadanda suka fito daga kasashen da aka samu bullar cutar”.

Ya kuma yi gargadi ga ‘yan kasar da kuma baki da su rinka tuntubar ma’aikatar lafiya idan suna da wata tambaya dangane da cutar ko yadda za su kare kansu.

Cutar dai na ci gaba da yaduwa tamkar wutar daji ind ko a ranar Litinin sai da aka bayar da rahoton cewa ta kashe wani mashawarci ga jagoran addinin kasar Iran Ayatollah Khamenei.

A ranar 27 ga watan Fabrairu ne Saudiyya ta sanar da hana maniyatta aikin Hajji da Umrah shiga biranen Makkah da Madina, a wani matakin hana yaduwar cutar coronavirus mai shafar numfashi.

Ma’aikatar harkokin waje ta Saudiyya ta kuma ce za ta hana ‘yan kasashen da aka tabbatar akwai cutar ko tana barazana ga kiwon lafiyar al’umma zuwa kasar.

Leave a Reply