Tijjani Ibrahim Gaya, na jam’iyyar APC da ke takarar sanata a Kudu maso Yammacin Jigawa, ya rasu.
Ya rasu a wata asibitin China a jiya Asabar.
Rahotanni na cewa sai da aka soma kwantar da shi a wani asibiti da ke Abuja bayan gano cewa yana da cutar huhu kafin daga bisani a fitar da shi zuwa China domin samun cikakkiyar kulawa.
Watanni uku kenan da marigayin ya lashe zaben fitar da gwani.
Gwamna Jigawa, Muhamamdu Badaru Abubakar, ya ce wannan babban rashi ne a garesu a wata sanarwar ta’aziya zuwa ga iyalansa.
Marigayin ya taba wakiltar mazabarsa ta Dutse/Kiyawa a majalisar wakilai tsakanin 2011 zuwa 2015.