Dan takarar gwamnan Jihar Zamfara a qarqashin inuwar Jam’iyyar APC, Dr. Dauda Lawal Dare (Gamjin Gusau) ya yi Allah wadai da yadda lamarin tsaro ke ci gaba da tabarbarewa a fadin Jihar Zamfara.
Dan takarar na jam’iyyar APC ya yi wannan Allah wadai da jimami ne a wata hira da Jaridar LEADERSHIP A Yau, inda ya bayyana irin baqin ciki da alhininsa ga wannan ta’asa ta ‘yan ta’adda a jihar Zamfara.
Ya bayyana aikin nasu da aiki na marasa imani da tausayi, tare kuma da yin kira ga gwamnatin Jihar ta Zamfara da ta san cewa nauyin kare rayuka da dukiyoyin al’umma sun rataya ne a wuyansu.
Sannan kuma Dan takarar na jam’iyyar APC, ya bayyana farin cikinsa matuqa ga ‘yancin da tagwayen nan suka samu, wadanda suka shafe kwanaki a hannun masu garkuwa, tare kuma da yin addu’ar Allah ya kubutar da sauran wadanda ke hannunsu.