Tsohon Kwamshinan Aikace-aikace na Jihar Kano, Mu’azu Magaji wanda aka fi sani da Dan Sarauniya ko Wini Win ya sanar da ficewarsa daga PDP.
Dan Sarauniya ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook, inda ya ce zai koma inda ya fito ne na asali.
Sai dai dan siyasar yana shan suka kan abin fa wasu suke bayyanawa a matsayin tsilla-tsilla da yawa da rashin akida.