BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Dan sanda ya kashe dan sanda a Kebbi

Rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi a Najeriya ta ce tana ci gaba da bincike kan mutuwar wani jami’inta ASP Shu’aibu Sani Malumfashi, bayan wani faɗa da takwaransa mai muƙamin ASP.

Rundunar ta ce, a ranar 19 ga watan Oktoban 2022, ne da rana jami’anta biyu da ke aiki a ofishinsu da ke Argungu wato ASP Abdullahi Garba, da kuma ASP Shu’aibu Sani Malumfashi, suka samu sabani kuma a dalilin haka ne suka kaure da fada.

Rundunar ta bakin jami’in hulda da jama’arta SP Nafi’u Abubakar, ta shaida wa BBC cewa, bayan jami’na ‘yan sandan sun kaure da fada ne sai ASP Abdullahi Garba, ya yi amfani da almakashi ya soki abokin aikin nasa a hakarkari.

SP Nafi’u Abubakar, ya ce bayan soka masa almakashin ne sai ya yanke jiki ya fadi kasa, anan ne DPO din da ke ofishin ya garzaya ya je wajen ya taradda abokin aikin nasu a kwance cikin jini anan ne aka kwashe shi aka kai asibiti.

Leave a Reply