Kano Ayau Hausa, Siyasa

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Kwankwaso, da wasu 3 sun fice daga NNPP zuwa APC

Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar mazabar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, Madobi, Kabiru Yusuf Isma’il ya sauya sheka daga jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP) zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Kano.

A wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya fitar ta bayyana cewa dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Dawakin kudu, Mu’azzam El-Yakubu, shi ma ya fice daga jam’iyyar NNPP ta Kwankwaso zuwa APC.

Yace a kwanakin baya guguwar sauya sheka ta mamaye jam’iyyar NNPP, musamman ‘yan majalisar jiha da na kasa.

Malam Garba yace tuni dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Bagwai da Shanono, Isa Ali ya koma jam’iyyar APC kwanaki bayan ya koma jam’iyyar NNPP.

Abokin aikin Garba a majalisar Jaha mai wakiltar mazabar Dambatta, Murtala Kore ya kuma fice daga jam’iyyar NNPP ya ci gaba da zama a jam’iyyar APC.

Leave a Reply