WASANNI

Dan Boksin Mayweather ya ba gurgu sadakar Naira dubu 360

Rahotannin da ke fitowa daga Amurka sun ce shahararren dan damben boksin din nan da asalin Amurka Flyod Mayweather ya yi sadakar Dala dubu 1, kimanin Naira dubu 360 ga wani gurgu da ke neman taimako a kan keken guragu a wani titi a Amurka.

Bayanin haka na kunshe ne a wani faifan bidiyo da dan boksin din ya watsa a shafin sadarwarsa na Instagram, inda aka nuna dan boksin din jim kadan da fitowarsa daga wani Otel da ya gina na kashin kansa ya ci karo da musakin, kuma ya mika masa kyautar Dala dubu.

Nan take musakin, wanda ba a bayyana sunansa da garin da ya fito ba ya yi yunkurin mikewa don ya rungumi Mayweather saboda murna, amma dan boksin din ya hana shi.

Gurgun wanda yake kwana a kan titi saboda rashin muhalli, ya nuna matukar farin cikinsa da ya samu wannan kyauta, kuma ya ce ko shakka babu hakan zai canja masa rayuwa.

Mayweather wanda ya yi ritaya daga yin damben boksin, a yanzu haka yana kokarin sake komawa ruwa ne inda yake kokarin sake karawa da dan boksin Manny Packuiao nan gaba kadan.

A bayanin da Mayweather ya rubuta a shafin sadarwarsa na Instagram ya ce “Ina farin cikin shaida wa duniya cewa na canja rayuwar wani mabukaci.”

Daga nan sai dan damben ya shawarci shahararrun ’yan wasa a Amurka irin su mai wasan barkwanci Kebin Hart da shahararren dan wasan kwallon kwando na kulob din LA Lakers Star Lance Stephenson da su yi koyi da shi wajen ba marasa galihu kyauta mai tsoka don su canja musu rayuwa.

Idan za a tuna a watannin baya ne Aminiya ta rubuta wani labari a kan Mayewather inda ya sayi agogon hannun da aka kiyasta kudinsa a kan Naira biliyan 6.

An shaidi Mayewather a matsayin mutumin da ke da sha’awar sayan kayayyaki masu tsada da suka hada da tufafi da motoci da takalma da riguna da agogon hannu da gida da sauransu.

 

Leave a Reply