BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Dan bindiga ya kashe mutum uku, ya raunata bakwai a Amurka

an sanda a Amurka sun ce wani mutum ɗauke da bindiga ya buɗe wuta kan wata sakandare a kudancin birnin St Louis da ke Jihar Missouri inda ya kashe aƙalla mutum biyu da kuma raunata aƙalla bakwai kafin yan sandan ƙasar su ma suka harbe shi har lahira.

Kwamishinan ƴan sanda na St. Louis ya shaida wa manema labarai cewa ɗan bindigan ya kashe wata mata ne da wata yarinya kamar yadda muka kalato daga BBC.

Haka kuma ya ce wanda ake zargin wanda ƴan sandan su ma suka harbe shi ɗan kimanin shekara 20 ne kuma ba a gano ko shi wanene ba.

Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa mutane da dama sun tsira ne sakamakon bindigar maharin da ta maƙale yana tsaka da harbi.

Leave a Reply