Kano Ayau Hausa, Manyan Labarai

Dalla-dalla: Abin da ya jawo yaki tsakanin Ukraine da Rasha

Ukraine da Russia kasashen turawa ne da suke bangaren gabas a nahiyar Turai, makwabta ne, suna kusa da juna sosai, al’adunsu kusan iri daya

Akwai wasu yankuna ko manyan birane wanda ake kira da Crimea, Luhansk, Donetsk da sauransu wanda suke yankin Arewa da kuma gabashin Kasar Ukraine akan iyaka da Kasar Russia, yankuna ne da suke fama da rikicin neman ‘yancin kai daga Ukraine, kuma yankin ya tara mutane ‘yan asalin Kasar Russia

Shugaban Kasar Ukraine Volodymyr Zelensky yana da ra’ayin kulla alaka da Amerika, domin har ya bayyana niyyarsa na shigar da Ukraine cikin kungiyar NATO (North Atlantic Treaty Organization) kungiyar hadin kan wasu kasashen turawa wanda Amerika ta kirkira bayan yakin duniya na biyu, akwai Kasashen Turawa talatin a cikin kungiyar NATO karkashin jagorancin Amurka wanda suke da rundinar tsaro na musamman da zasu iya kalubalantar barazanan tsaro

Sannan akwai kungiyar kasashen turawa G7 (Group of Seven) masu karfin tattalin arziki a Turai wanda ya hada kasashen Amerika, Ingila, Faransa, Italiya, Japan, Germany da Kanada, sun hadu sun kafa kungiyar G7 (Group of Seven) domin su samu cikakken hadin kai a bangaren tattalin arziki, siyasa da kuma tsaro, to shi shugaban Kasar Ukraine mai makwabta da Russia yana son ya shigar da Kasar cikin kungiyar NATO da G7

Ukraine Kasace ko wani yanki ne da ya taba zama karkashin mulkin Gwamnatin tsohuwar tarayyar Soviet (Russia), musamman bangaren gabas da Arewacin Ukraine inda ake fama da rikici a yanzu, to bayan kasashen duniya sun karya Gwamnatin Soviet a wancan lokaci sai Russia ta jagoranci kafa rundinar soji na musamman na kungiyar hadin kan kasashe masu manufa irin nata, wato Collective Security Treaty Organization (CSTO), akwai Kasashe kamar haka Russia, Armenia, Uzbekistan, Kazakhstan, Georgia, Azerbaijan da sauransu

Wato yadda Amerika ta jagoranci wasu kasashen turai aminanta wajen kafa kungiyar NATO to kamar hakane Kasar Russia ta jagoranci kawayenta suka kafa kungiyar CSTO, kasashen NATO da CSTO basa shiri da juna sam, Ukraine tana kan iyaka da Russia, to sai ya zama shugaban Ukraine yana son ya shigar da Kasar cikin NATO da G7, shi kuma shugaban Russia yana ganin hakan a matsayin wata babban barazana da kuma takalar yaki idan aka wayi gari makwabciyar kasarsa ta shiga NATO, saboda a duniya ba Kasar da Russia take gaba da ita kamar Amerika

Tun a shekarar 2014 shugaban Kasar Russia Vladimir Putin ya bawa yankin Crimea dake Kasar Ukraine ‘yanci wanda hakan shine mafarin yaki tsakanin kasashen da suke makwabta da juna, a farkon wannan satin sai aka wayi gari rana tsaka Shugaban Kasar Russia ya sake bayyana wasu yankuna da suke gabashin Ukraine wato Luhansk da Donetsk a matsayin kasa mai cin gashin kanta, wato ya ‘yanta yankin daga Kasar Ukraine, sai ya tura dubbannin sojoji kimanin dubu dari da hamsin zuwa yankin da suke cikin Ukraine da sunan zasuyi aikin kwantar da tarzoma da kuma bada cikakken kariya wa ‘yan asalin Kasar Russia da suke yankin

To ita kuma Kasar Ukraine da babbar kawarta Amerika sai suka kalli hakan a matsayin wata babbar barazana da shirin takalar yaki, domin abinda Amerika take kalla shine Russia tana shirin mamayar Kasar Ukraine ne gaba daya, to wannan ne ya jawo halin da ake ciki yanzu har Russia ta kaddamar da harin makamai masu linzami a babban birnin Ukraine

Yanzu haka shugaban Kasar Ukraine yana kira ga Kasashen duniya su kawo masa dauki, kuma yace duk wani ‘dan kasar ya saka kakin soji a fito ayi yaki, sai dai da alama ya hadu da yauran Kasar Amerika, abin mamaki Amerika ta gagara mayar da martani, ko bawon gyada bata bare ba don aji kara bayan Russia ta kaddamar da hari kan Ukraine, wato kamar za’a ce Amerika ta yaudari Ukraine da zakin baki da kuma farfaganda

Domin ba shakka Amerika ko da wasa bata isa ta takali Russia da yaki ba saboda tsoron abinda zai biyo baya, kuma manyan kasashe aminan Kasar Russia irin China da North Korea ba zasu kyale ba, suma zasu marawa Russia baya, idan Amerika tayi gangancin amfani da makami to hakan zai iya jefa duk kasashen duniya cikin rigimar yaki da karayar tattalin arziki

Muna rokon Allah Ya sa yakin da suke neman tayarwa a duniya ya kare a kansu

Daga Arewa Intelligence

Leave a Reply