BABBAN BANGO, Kano Ayau Hausa

Dalilin da ‘yan sanda suka kama Ali Madaki

Rundunar ƴan sandan jihar Kano ta gayyaci sabon Ɗan Majalisar Tarayya na ƙaramar hukumar Dala, Ali Sani Madakin Gini na Jami’yyar NNPP, bisa zargin mallakar Bindiga ba bisa ƙa’ida ba.

A sanarwar da Kakakin Ƴansandan Kano SP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ya ce, Madakin na tsare a sashen binciken manyan laifuka da ke Bompai.

A yan kwanakin nan dai an yita yaɗa wasu hotunan Madakin rike da bindiga a kafafen sada zumunta.

Tsare Ali Madaki na zuwa ne kwana guda bayan da jami’an tsaro suka cafke Ɗan Majalisar Tarayya na Tudunwada da Doguwa kuma shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alhassan Ado Doguwar bisa zargin ta da hargitsi da kisan kai, inda suka kai shi Kotu.

Leave a Reply