Big Story, Kano Ayau Hausa, Labarai

Dalilin da na yi karya an yi garkuwa da ni-Amirah

Amirah Sufyan ta ce karya ta yi cewa an yi garkuwa da ita a kwanakin baya.

Amirah ta bayyana hakan ne a wajen ’yan sanda, inda ta ce kasarci ne kawai ya sa ta yin hakan.

A cewarta, da kanta ta fita daga gidansu, ta shiga dajin, sannan ta rika wallafa cewa an yi garkuwa da ita ne.

A karshe ta nemi afuwar mutanen gari, da ’yan sanda da ’yan uwanta da abokan arziki da mutanen gari baki daya.

A makon jiya ne aka ruwaito an yi garkuwa da Amirah daga Abuja, an tafi da ita Jos, inda daga cikin dajin ta rika wallafa a shafin Twitter cewa tana waje kaza, wanda hakan ya sa mutane suka ta cewa ’yan sanda da sauran jami’an tsaro ba su iya aiki ba tunda har za su kasa ceto ta duk da cewa ta sanar da inda take.

Hakan ya sa ’yan sanda suka mike wajen bibiyan lamarin, har suka kai ga dauko ta.

Leave a Reply