GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Dalilin da ake fuskantar rashin wuta-Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Najeriya ta ce an samu matsala ne a babban layin samar da lantarki na ƙasa.

Wata sanarwar daga ofishin ministan lantarki na Najeriya Injiniya Abubakar Aliyu ta ce ana gudanar da bincike domin gaggauta magance matslar.

An fuskanci katsewar lantarki a sassan Najeriya a ranar Juma’a.

Sanarwar ta ce: “muna sanar da al’umma cewa matsalar ta faru ne karfe 18:30 a ranar 8 ga Afrilu, wanda ya haifar da matsalar lantarki a sassa da dama na ƙasa,” kamar yadda BBC ta ruwaito.

Leave a Reply