Kuɗi ne kawai ke aiki a zaɓen fidan takarar gwamna wamnan a jam’iyar PDP a Jihar Kano, ɓangaren Ambasada Aminu Wali, Muaz Magaji, wanda a ka fi sani da Dansarauniya, ya bayyana cewa anyi amfani da kuɗi wajen zaɓen fidda-gwani da a yanzu haka a suka gudanar a cibiyar Wasa ta Sani Abacha.
Dansarauniya ya bayyana hakan ne a Sahihin shafinsa na Facebook a safiyar ysu Alhamis.
Tun da fari dai Dansarauniya ya ke yabo da nuna shauƙi kan yadda zaɓen ke tafiya.
Amma kuma da a ka zo ɓangaren irgen ƙuri’u, sai ya wallafa a shafin da na facebook cewa kuɗi ne kawai ke aiki a zaɓen.
“An fara irgen ƙuri’u… ta bayyana dai kuɗi ne ke aiki. Allah ya zaɓa mana alheri,” in ji shi.
“mun gwada shiga tsarin mun kuma ga yadda yake, amma dai da alama lokacinmu baiyi ba.
“Mun fafata, amma Banu samu nasara ba. Dama mun shiga takarar ne a mutunce da kuma girma. Amma dai ba mu ƙara ta’azzara matsalar lalacewar harkar zaɓe a ƙasar nan ba, sai dai kawai mun shiga ne domin mu gwada sa’ar mu,” a cewar Dansarauniya.
A Jiya ne dai jam’iyyar PDP ta gudanar da zaben fidda gwani na kujerar gwamna har sau biyu da tsagin Aminu Wali sukai Masu daban su ma tsagin Shehu wada Sagagi sukai nasu daban.
Tuni dai tsagin su Shehu wada Sagagi sukai tsayar da Muhammad Abacha a matsayin wanda zai yi musu takara, su kuma tsagin su Aminu Wali har yanzu kirga kuri’u ake yi basu kai ga bayyana wanda yayi nasara ba.