GAJERAN LABARI, Kano Ayau Hausa

Cutar Covid-19 ta kusa zama tarihi-WHO

Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce tsawon saura kiris duniya ta ga bayan cutar COVID-19.
Ya ce sati biyu ke nan da ake samu mafi karancin adadin wadanda suka kamu da cutar tun bayyanarta a shekarar 2019
Shugaban ya bayyana hakan ne ga manema labarai ranar Laraba, inda ya yaba wa kasashen duniya kan kokarinsu da ya kai ga cim ma wannan nasara.
A cewarsa, “Idan ba mu yi amfani da wannan damar ba, to za a kuma samun yaduwar wasu nau’ukan da mace-mace da rashin tabbas.

“Mun samar da wasu dokoki guda shida da za su taimaka wa kasashen duniya kawar da cutar baki daya, har ma da wasu bala’o’i da za a iya samu nan gaba,” kamar yadda Aminiya ta ruwaito.

Leave a Reply